John 4

Yesu Ya Yi Magana da Wata Basamariya

1Sai Farisiyawa suka ji cewa Yesu yana samun yana kuma yi wa almajirai da yawa baftisma fiye da Yohanna, 2ko da yake ba Yesu ne yake baftismar ba, sai almajiransa.

3Da Ubangiji ya sami wannan labari, sai ya bar Yahudiya ya sāke koma Galili.

4To, ya zama dole yǎ bi ta Samariya. 5Sai ya zo wani gari a Samariya da ake ce da shi Saikar, kurkusa da filin da Yaƙub ya ba wa ɗansa Yusuf. 6Rijiyar Yaƙub kuwa tana can, Yesu kuwa, saboda gajiyar tafiya, sai ya zauna a bakin rijiyar. Wajen saʼa ta shida ne.

7Saʼad da wata Basamariya ta zo ɗiban ruwa, sai Yesu ya ce mata, “Za ki ba ni ruwa in sha?” 8(Almajiransa kuwa sun shiga gari don sayi abinci.)

9Sai Basamariyar ta ce masa, “Kai Bayahude ne ni kuwa Basamariya ce. Yaya za ka roƙe ni ruwan sha?” (Don Yahudawa ba sa hulɗa da Samariyawa).

10Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah da kuma wanda yake roƙonki ruwan sha, da kin roƙe shi, da shi kuwa ya ba ki ruwan rai.”

11Sai macen ta ce, “Ranka yǎ daɗe, ba ka da guga rijiyar kuwa tana da zurfi. Ina za ka sami wannan ruwan rai? 12Ka fi mahaifinmu Yaƙub ne, wanda ya ba mu rijiyar ya kuma sha daga ciki da kansa, haka ma ʼyaʼyansa da kuma garkunan shanunsa da tumakinsa?”

13Yesu ya amsa, ya ce, “Kowa da ya sha wannan ruwa zai sāke jin ƙishirwa, 14amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi ba zai ƙara jin ƙishirwa ba. Lalle, ruwan da zan ba shi zai zama maɓuɓɓugan ruwa a cikinsa da yake ɓuɓɓugowa har yǎ zuwa rai madawwami.”

15Sai macen ta ce masa, “Ranka yǎ daɗe, ka ba ni ruwan nan don kada in ƙara jin ƙishirwa in yi ta zuwa nan ɗiban ruwa.”

16Sai ya ce mata, “Je ki kira mijinki ki dawo.”

17Ta ce, “Ai, ba ni da miji.”

Sai Yesu ya ce mata, “Gaskiyarki da kika ce ba ki da miji.
18Gaskiyar ita ce, kin auri maza biyar, mutumin da kike da shi yanzu ba mijinki ba ne. Abin da kika faɗa yanzu gaskiya ne.”

19Sai macen ta ce, “Ranka yǎ daɗe, na gane kai annabi ne. 20Kakanninmu sun yi sujada a kan dutsen nan, amma ku Yahudawa ɗauka cewa inda ya kamata mu yi sujada shi ne Urushalima.”

21Sai Yesu ya ce, “Ina tabbatar miki, mace, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ko a kan dutsen nan ko kuma a Urushalima ba. 22Ku Samariyawa kuna yi wa abin da ba ku sani ba sujada; mu kuwa muna yi wa abin da muka sani ne sujada, gama ceto daga Yahudawa yake. 23Duk da haka lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada cikin Ruhu da kuma gaskiya, domin irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema. 24Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada cikin ruhu da kuma cikin gaskiya.”

25Macen ta ce, “Na san cewa Almasihu, (da ake ce da shi Kiristi) yana zuwa. Saʼad da ya zo kuwa, zai bayyana mana kome.”

26Sai Yesu ya ce, “Ai, ni ɗin nan da yake magana da ke, Ni ne shi.”

Almajirai Sun Dawo Inda Suka Bar Yesu

27Nan take sai almajiransa suka dawo suka kuma yi mamakin ganinsa yana magana da mace. Amma ba wanda ya ce, “Me kake so?” Ko “Me ya sa kake magana da ita?”

28Sai macen ta bar tulunta na ruwa, ta koma cikin gari ta ce wa mutane, 29“Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi. Shin, ko shi ne Kiristi?” 30Sai suka fito daga garin suka nufo inda yake.

31Ana cikin haka almajiransa kuwa suka roƙe shi suka ce, “Rabbi, ci wani abu.”

32Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku sani ba.”

33Sai almajiran suka ce wa juna, “Shin, ko wani ya kawo masa abinci ne?”

34Yesu ya ce, “Abincina shi ne, in aikata nufin wannan da ya aiko ni, in kuma gama aikinsa. 35Ba kukan ce, ‘Sauran wata huɗu a yi girbi ba?’ Ina gaya muku, ku buɗe idanunku ku dubi gonaki! Sun isa girbi. 36Ko yanzu ma mai girbi yana samun ladansa, ko yanzu ma yana girbin amfani domin rai madawwami, saboda mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare. 37Karin maganan nan gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani kuma da girbi.’ 38Na aike ku girbin abin da ba ku yi aikinsa ba. Waɗansu sun yi aikin nan mai wahala, ku kuwa kun sami ladan aikinsu.”

Samariyawa da Yawa Sun ba da Gaskiya

39Samariyawa da yawa daga wannan gari suka gaskata da shi saboda shaidar macen da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.” 40To, da Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roƙe shi yǎ zauna da su, ya kuwa zauna kwana biyu. 41Saboda kalmominsa kuwa da yawa suka gaskata.

42Sai suka ce wa macen, “Yanzu kam mun gaskata, ba don abin da kika faɗa kawai ba; yanzu mun ji da kanmu, mun kuwa san cewa wannan mutum tabbatacce shi ne Mai Ceton duniya.”

Yesu Ya Warkar da Ɗan Mai Mulki

43Bayan kwana biyun nan sai ya bar can zuwa Galili. 44(To, Yesu kansa ya taɓa faɗa cewa annabi ba shi da daraja a ƙasarsa). 45Da ya isa Galili, sai mutanen Galili suka marabce shi. Sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin Bikin Ƙetarewa, gama su ma sun kasance a can.

46Sai ya sāke ziyarci Kana ta Galili inda ya juya ruwa ya zama ruwan inabi. Akwai wani maʼaikacin hukuma a can wanda ɗansa yake kwance da rashin lafiya a Kafarnahum. 47Da mutumin nan ya ji cewa Yesu ya isa Galili daga Yahudiya, sai ya je wurinsa ya roƙe shi yǎ zo yǎ warkar da ɗansa da yake bakin mutuwa.

48Yesu ya ce masa, “Ku mutane, in ba kun ga alamu da abubuwan banmamaki ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.”

49Maʼaikacin hukuman ya ce, “Ranka yǎ daɗe, ka zo kafin ɗana yǎ mutu.”

50Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Ka tafi. Ɗanka zai rayu.”

Mutumin kuwa ya amince da maganar da Yesu ya yi ya kuwa tafi.
51Tun yana kan hanya, bayinsa suka tarye shi da labari cewa yaron yana warkewa. 52Da ya tambayi lokacin da ɗansa ya sami sauƙi, sai suka ce masa, “Zazzaɓin ya sake shi jiya a saʼa ta bakwai.”

53Sai mahaifin ya gane a daidai wannan lokaci ne Yesu ya ce masa, “Ɗanka zai rayu.” Saboda haka shi da dukan iyalinsa suka gaskata.

54Wannan ce abin banmamaki ta biyu da Yesu ya yi, bayan zuwansa daga Yahudiya zuwa Galili.

Copyright information for HauSRK